@trtafrikaha: Matashiyar tauraruwar finafinan Kannywood Fatima Hussaini Abbas ta ce halayenta a cikin shirin 'Labarina' su ne kusan halayenta na zahiri domin kuwa “ba na soyayya domin kudi”. A hirarta da TRT Afrika Hausa, tauraruwar wadda aka fi sani da Maryam a 'Labarina', ta ce za ta iya auren talaka idan har tana kaunarsa. “Ba wai ina nufin ihsani ba shi da dadi ba ne. Amma ba na son mutane don abin da suka mallaka ko abin da za su ba ni” in ji ta.#labarina #arewa__tiktok #hausatiktok #kannywood