@galadimapalaceenterprise: Assalamu Alaikum Cikin ikon Allah, Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nada Imam Hassan Dr. Mukhtar Atamma Fagge matsayin wanda zai gabatar da Karatun Azumin bana 1446/2025 na kullum kullum, a fadar gidan Sarki ta Nasarawa. Za a karanta Littafin ASSHIFA na Alkali Iyadh (RA) na tsawon kwanaki talatin (30). Za a fara wannan karatu kamar haka: Rana: Asabar 1 ga Ramadhan 1446. 1/ March 2025. Lokaci: 09:00 am zuwa 10:30 am. Wuri: Fadar Mai Martaba Sarki ta gidan Nasarawa. Allah ya saka wa Mai Martaba Sarki da alkhairi, ya ji kan Sarkin Kano Alh. Ado Bayero. Allah ya kara wa Dr. Mukhtar Atamma kusanci da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Allah ya sa a fara lafiya, a gama lafiya.