@abunasreen_jega: A Aljannah, zaka fahimci yadda damuwar da ta dabaibaye zuciyarka a duniya ta kasance ƙarama kuma abar banza. Kuma idan ka tsaya a bakin fadar ka, ka kalli fāɗinta mai ban mamaki da hasken da ke fita daga cikinta — zaka tabbatar da cewa duniya ba ta da wani ƙima kwata-kwata! Idan ka ji wannan kira yana tashi: "Ya mazaunan Aljannah! Rayuwa ce ba mutuwa!" Zuciyarka zata natsu, ka san cewa dukan fuskar da kake gani ba za su taɓa rabuwa da kai ba har abada — babu mutuwa, babu ɓaraka! A Aljannah… ba za ka taɓa ganin wanda ke cikin baƙin ciki ko damuwa ba. Ba za ka taɓa shiga taro da ake gulma ko ƙarya ko cin mutunci ba! A Aljannah… dukkan zukata tsarkakku ne — babu hassada, babu ƙiyayya, babu makircin zuciya! A Aljannah… ba za ka sake jin raɗaɗin abubuwan da suka wuce a duniya ba. Baƙin ciki, damuwa, ciwo — duk za su ɓace a daƙiƙar farko da ka shiga Aljannah! Aljannah! Ita ce ƙaunar da duniya ta gaza bayarwa. Ita ce farin cikin da duniya ba ta iya ɗaukarsa. Ita ce ƙarshe ga duk abin da aka haramta da aka hana a duniya. Ita ce ƙarshen gajiya, ƙarshen gundura, ƙarshen yanke ƙauna. Aljannah... ita ce mutuwar mutuwa! Idan kana kewar Aljannah irin yadda baƙo ke kewar ƙasarsa — to ka yi aiki domin samun wannan ni’ima mai girma! Ya Allah! Ka bani da ku wannan babban ni’ima, Ka ba mu YardarKa da AljannarKa. Ameen.🌹 #abunasreenjega #aljannah #taqwa #foryou

Sirrin GIDAN AURE 🌹
Sirrin GIDAN AURE 🌹
Open In TikTok:
Region: NG
Wednesday 04 June 2025 20:04:52 GMT
2539
115
1
7

Music

Download

Comments

wasila.ta.annabi
wasila ta annabi :
💕💕💕
2025-06-05 17:28:19
1
To see more videos from user @abunasreen_jega, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About