@dahirmhashim: A jawabi na, na jaddada cewa sauyin yanayi ba barazana ce ta nesa ba, barazana ce da muke fuskanta kullum wadda ke shafar jadawalin noma, albarkatun ruwa da kuma tsaron abinci. Na bayyana yadda mu a Kano muke ɗaukar matakai ta hanyar shuka bishiyoyi, ayyukan magance ambaliya, yin takin gargajiya daga shara da kuma dawo da ƙasar data lalace saboda zaizayar ƙasa. Waɗannan ba ayyukan wucin gadi ba ne, su ne ginshiƙin da manoma za su iya tsara harkokinsu, saka jari da kuma haɓaka, a yanayin da yake canzawa. Na kuma jaddada rawar da matasa manoma ke takawa wajen inganta noman da ya dace da yanayi. Ta hanyar daukar matakan da ke kare lafiyar ƙasa, amfani da ruwa yadda ya kamata, rage ɓarnar amfanin gona da kuma dashen bishiyoyi cikin gonaki, za su iya tabbatar da abinci, samar da ayyukan yi da kuma kare muhalli. A matsayina na wakilin gwamnati, zamu dage wajen tallafa musu da tsare-tsare, haɗin gwiwa, da shirye-shiryen da za su bai wa matasa damar yin noma mai dorewa. Dr. Dahir M. Hashim Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano

Dr. Dahir M. Hashim
Dr. Dahir M. Hashim
Open In TikTok:
Region: NG
Sunday 07 September 2025 20:16:06 GMT
941
138
10
1

Music

Download

Comments

sanee1992
SaniHharbau :
ga matsalar #zaizayarkasa nan ko ina amma kungagara daukar matakan da suka dace
2025-09-08 11:57:58
1
ibraheem_musah
Amib_International :
Fatan nasara 👏
2025-09-07 22:22:38
1
abdulabdul08186
Abdul Abdul :
masha Allah
2025-09-07 20:42:26
1
bilya.ahmad
Bilya Ahmad Rurum :
Muna maka fatan alkhairi Muna matukar alfahari da kai Allah ya tsare maka mutuncin ka
2025-09-07 20:50:00
1
abdulazizibrahim299
abdulazizibrahimali299 :
Allah yayiwa rayuwa albarka boss Dahir 🙏
2025-09-08 04:49:30
1
abdurrahamandalhatu066gm
Abdurrahaman dalhatu :
Allah ya cigaba da taimakon ka uban gidan fita kunya muna godiya da abun Alheri
2025-09-10 17:24:22
0
saratumuhammad18
saratumuhammad981 :
Allah yaqadaukaka Allah yatsareka ameeen ya Allah
2025-09-22 17:36:51
0
saidusani861
Dan saidu :
masha Allah
2025-09-11 06:51:36
0
saratumuhammad18
saratumuhammad981 :
yarana biyune marayu dan Allah kataimakamin koda makarantarsune dan Allah zasuje sakandiri wlh banida hali nimacece kuma banida jari shiyasa
2025-09-22 17:40:37
0
umarbashir678
umarbashir678 :
@Dr. Dahir M. Hashim mai girma dr. Dan allah a duba koken unguwar janbulo 1 gate. Wlh sharar nan nema take ta hanayin maulidin annabi saw.
2025-09-07 22:53:42
1
To see more videos from user @dahirmhashim, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About