@khamis_ali_m_abdullah: Wane amfani wayarka take maka a yau? Shin ka taba tunanin irin ni’imar da kake ciki ta samun ilimi cikin sauki? 1- Kana iya sauraron karatu kana tsaye. 2- Kana iya sauraron karatu kana zaune. 3- Kana iya sauraron karatu har ma kana kwance. Duk yadda kake so, ilimi yana nan a tafin hannunka Darasi Daga Magabata Magabatanmu sun sadaukar da rayuwarsu wajen neman ilimi duk da tsananin wahalhalu. Akwai dalibin da zai bar gidansa ya tafi wata kasar domin karatu ba ya damuwa da yanayin shimfida ko dakin da zai kwana, babban burinsa kawai shi ne ya samu abin da ya kaita (wurin karatu) Kawai don ba a kwana a makarantar ne yake neman wurin kwana! Sakonmu a yau Ilimi ya zo gare mu har gida, amma ko muna amfani da damar? Kar mu bari wayoyinmu su zama abin wasa kawai, yayin da za su iya zama silar daukakarmu a duniya da lahira. Professor Mansur Isa Yelwa (Hafizahullah) #professormansuryelwa #khamis_a_m_abdullah