@katieharris6966: #disturbing #caughtoncamera #scarytiktoks #fyp #shocking

katieharris6966
katieharris6966
Open In TikTok:
Region: US
Saturday 28 February 2026 04:10:17 GMT
398
16
0
0

Music

Download

Comments

There are no more comments for this video.
To see more videos from user @katieharris6966, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos

GYARA KAYANKA BAI ZAMA DALILIN RABA MU BA! Na san za ku tuna da dambarwarmu da ’yan Izala kan batun kiran Kiristoci da sunan “Arna” da kuma buƙatar daina amfani da wannan kalma domin kiyaye zaman lafiya. A cikin wannan faretin, ana cewa: “A ba ni AK!” Na je Enugu, a cikin “arna”, suna tafi, suna murna, na ba su wuta. Amma abin da nake nufi ba wai komai ba ne illa a daina kiran Kiristoci da sunan “arna” a tsarin dimokuraɗiyya da zaman tare, domin irin wannan salon magana na iya haifar da ƙiyayya da rarrabuwar kai, maimakon gina zaman lafiya. Hakika, Musulmi na gari bai kamata ya kasance mai ƙiyayya ba, domin ƙiyayya cuta ce da ke lalata zamantakewa. Saboda haka, ku masu sukar Izala saboda sabanin fahimta, ku ma ku ji tsoron Allah. Ku sani cewa ba dukkansu ne suke da irin wannan mummunar ɗabi’a ba. A ganina, wasu daga cikin ’yan Izala a Kaduna suna nuna kyakkyawan misali wajen wayewa da fahimtar zamantakewa, yayin da wasu daga cikinsu a Jos suke nuna tsaurin ra’ayi da ƙiyayya a ƙarƙashin inuwar saɓanin fahimta da abokan zama. Abin da nake ƙoƙarin bayyanawa shi ne, addini bai kamata ya zama hujjar zaluntar wanda ba ya bin addininka ba, ko kuma a jingina masa barna saboda bambancin addini. Ya zama wajibi mu riƙa rayuwa bisa matsakaiciyar hanya (Wasadiyya), kamar yadda Allah Ya koyar da mu. Ya ku waɗanda ba Musulmi ba, ku ji tsoron Allah, ku daina yi wa Musulmi kallon cewa dukansu iri ɗaya ne. Ku sani cewa a cikinmu akwai masu ƙoƙarin kare ’yancinku da mutuncinku. Ni kuwa, na barranta daga duk wani tsattsauran ra’ayi da ake yi wa mutane da sunan addini. Mu zama ƙasa ɗaya, al’umma ɗaya! Allah Ya haɗa mu a kasuwanni, makarantu, wuraren aiki da sauran harkokin rayuwa. Saboda haka, ya kamata kowa ya mutunta doka, ya kuma yi aiki da kyawawan ɗabi’un da addininsa ya koyar da shi. ’Yan Izala: Ku guji taƙalidanci da ta’assubanci. ’Yan Shi’a: Ku guji tsattsauran ra’ayi, ku yi ƙoƙarin bin koyarwar Alƙur’ani da ingantacciyar Sunnah bisa fahimtar da ta dace. ’Yan Ɗarika: Ku guji duk wani abu da ya saɓa wa koyarwar Manzon Allah (SAW), ku kuma mayar da hankali kan bin Sunnarsa da ingantattun hujjoji. ’Yan Qalaqato: Ku yi ƙoƙarin tabbatar da cewa ayyukanku sun dace da koyarwar addininku. Ku kuma Kiristoci: Ina kira gare ku da mu ci gaba da zama cikin zaman lafiya, mutunta juna da haɗin kai, duk da bambancin addininmu. A ƙarshe, mu tuna cewa bambancin addini bai kamata ya zama sanadin ƙiyayya, zalunci ko rarrabuwar kai ba. Mu gina ƙasa bisa adalci, mutunta juna da zaman lafiya. Allah Ya sa mu zauna lafiya, Ya haɗa kan al’ummarmu, Ya kuma shiryar da mu zuwa ga gaskiya. Amin!

About