@feedieskitchen: 🟢 Amfanin Chia Seed da Lemon wajen rage kitsen ciki 1. Yana sa ka koshi na dogon lokaci Chia seed na dauke da fiber mai yawa. Idan aka jika shi da ruwa yana kumbura, hakan yana rage yawan cin abinci. 2. Yana gyara narkewar abinci Yana taimakawa wajen sauƙaƙa bayan gida da rage kumburin ciki (bloating), wanda ke sa ciki ya ragu a gani. 3. Yana rage kwadayi (cravings) Yana taimakawa wajen daidaita sugar a jiki, hakan yana rage yawan jin yunwa ba tare da lokaci ba. 4. Yana kara ruwa a jiki (hydration) Shan wannan hadin yana taimakawa jiki samun ruwa sosai, wanda ke taimakawa metabolism. 5. Lemon yana kara anfani Lemon na dauke da vitamin C wanda ke taimakawa narkewar abinci da kuma rage kiba kadan. 6. Yana rage kumburin ciki Yana taimakawa cire ruwa da kumburin da ke sa ciki ya fito. ⸻ 🥤 Yadda ake hada shi • Cokali 1 na chia seed • Kofi 1 na ruwan dumi • Ruwan rabin lemon Mataki: 1. A jika chia seed a ruwa na minti 10–15 2. A zuba ruwan lemon 3. A juya sosai sannan a sha ⸻ ⏰ Yadda ake sha • A sha da safe kafin a ci komai • Ko minti 30 kafin cin abinci