@salaahamedia_tv: Yawaita kallon fina-finan Hausa ba tare da kula da ibada da neman ilimin addini ba na daga cikin abubuwan da ke jawo raunin tarbiyya da nisantar zuciya daga ambaton Allah. A cikin wannan muhimmiyar nasiha, malama ta yi bayani mai zurfi kan yadda wasu mata suke bata lokaci awanni wajen kallon fina-finai, alhali sun manta da karatun Alƙur’ani da bitar hadisai waɗanda su ne hasken rayuwa da gyaran zuciya. Wannan saƙo gargadi ne ga duk mai neman gyara da rabauta a duniya da lahira. Ku saurara ku anfani, sannan ku yada domin sauran ‘yan uwa su amfana.