@upbarcelona31: YANZU-YANZU: Barcelona ta cimma yarjejeniya da Julian Alvarez akan kwantaragin da zai kai har zuwa shekarar 2031, tare da zaɓin tsawaitawa har zuwa 2032. Albashin da aka tsara masa ya kai kusan €18.5m duk shekara harda garaɓasa. Barcelona dai ta shirya €100m jumulla domin siyan ɗan wasan gaban, yayin da Atlético Madrid ke neman €150m. Komai zai kammala nan ba da jimawa ba saboda Atletico Madrid suna son samun makwafinsa da wuri.