@mubeedabai: Mai Girma Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa, Alhaji Dauda Kahutu Rarara, ya ziyarci mahaifarsa ta Garin Kahutu domin ganin da idonsa yadda aka fara aikin tituna guda shida a cikin garin, waɗanda ya ɗauki alƙawarin aiwatarwa da kansa domin ci gaban al’umma. Bayan haka, ya kai ziyara wajen aikin Gadar Barmo, wacce ake sa ran za ta lashe miliyoyin kuɗaɗe, domin duba yadda aikin ke gudana da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da shi yadda ya kamata. Allah Ya sa a kammala waɗannan ayyuka cikin nasara, Ya sanya su zama alheri da cigaba ga al’ummar Garin da ma baki ɗaya. 🤲🏽✨🏗️