@dokinkarfetv: Duk Kwankwasiyya Ba Wanda Kwankwaso Zai Ba Wa Takara Ya Iya Ja Da Abba Ya Samu Rabin Ƙuri'un Da Abba Zai Samu, In Ji Mai Magana Da Yawun Gwamnan Jihar Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa Ya ƙara da cewa "Kwankwaso ya yi shirin haɗa kai da ƴan majalissa su tsige Gwamna Abba idan ya koma APC, amma bai yi nasara ba. Kuma, Billahillazi La'ilaha'illahuwa ko a watan Mayun da ya gabata sai da gwamnatin Kano ta yi wa Kwankwaso hidima ta kuɗaɗe". In ji kakakin gwamnan, ta cikin shirin Podcast na Dokin Ƙarfe TV. A dakace mu, cikakkiyarar firar na nan tafe a Youtube Channel ɗinmu na Dokin Ƙarfe TV, nan gaba kaɗan. #kwankwasiyya #abbagidagida #kano #apc #abuja