@_king_shameer: "ƴar tsohon shugaban ƙungiyar Boko Haram a Najeriya Abubakar Shekau wato Fatima Abubakar Shekau ta fito ta koka wa jama'a kan halin da take ciki na rashin samun mijin aure." Fatima wacce a yanzu haka take cikin shekarun ƙuruciyarta ta ce tana fuskantar tsangwama iri-iri daga wajen mutane, musamman idan aka tuna da mahaifinta wanda hakan ya sa rayuwa ta yi mata ɗaci. A shekara 2009 ne dai mahaifin nata ya karbi ragamar Boko Haram lamarin da ya sa aka sha gwagwarmaya da shi wajen yaƙi da gwamnati kan abin da ya kira kawar da gwamnatin yahudawa. Labarin mutuwarsa ya yi ta karaɗe shafukan sada zumunta sau da dama duk da yake yana fitowa daga bisani yana karyata hakan. Sai dai tun bayan da aka sake sanar da mutuwarsa a 2021 sakamakon artabu da dakarun sojin Najeriya, har kawo yanzu ba a sake jin motsinsa, lamarin da ya gaskata mutuwar tasa a wannan karo. A yanzu haka dai Fatima ta ce a shirye take ta raya Sunnar Manzon Allah SAW da zarar ta samu wanda zai riketa tsakani da Allah a rayuwa. Me zakuce ? #foryou #viral #BillionViewsChallenge #viralvideo #15MillionAudition