@marke.herbal.medicine: AMFANIN GANYAN MANGURO: Ganyen Mangwaro ya kunshi sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam wajen kawar da wasu cututtuka da suka saba addabar al’ummar musamman a wannan zamani. Ire-iren wannan sunadarai sun hada da: - Alkaloids - Phenols - Flavonoids - Saponins - Tannins - Calcium - Magnesium - Potassium - Phosphorus - Sodium - Copper - Zinc - Cadmium - Ascorbic acid - Riboflavin - Niacin - Thiamine A sakamakon wannan arziki na sinadarai da Allah yayiwa ganyen mangwaro Yana maganin wadannan cututtukan: 1- Ciwon Suga Ganyen mangoro yana daidai ta suga, sabida yana dauke da sinadarai masu saka jiki ya saki insulin. Ana iya jika ganyen magwaro a cikin ruwa ya kwana sai ayi amafani da shi yana taimaka wajen daidai ya suga. Haka Kuma za'a iya barin sa ya bushe sannan a maida shi gari adinga amfani dashi domin daidai ta suga. 2- Hawan Jini Kasancewar ganyar mangiro yana dauke da sinadaran vitamin hakan zaisa ya kona cholesterol mara amfani a jikin mutum, sannan ya daidai ta jinin mutum. 3. Matsalarar Koda Ana dafa ganyan mangoro kamar shayi a dinga sha da safe a matsayin abincin farko yana kawar da matsalar Koda, kuma yana narkar da tsakuwar koda tare da tsarkake ta daga cututtuka. 4- Matsalar Kirji ( Respiratory Track Infection) Ana iya dafa ganyan mangoro kamar shayi sannan a saka zuma a ciki ana amfani da shi ya saukake matsalar tari da rike kirji. 5- Cutar Atini Akan kwankwadi garin ganyen Mangwaro da aka jika da ruwa wajen samun waraka daga cutar atini ko da kuwa mai zuwa ce da fitar jini.