@azlanbestmodernfashion: Duk wanda ya gina farin cikinsa a kan yabon mutane, zai yi baƙin ciki idan suka daina yaba masa. Amma wanda ya gina darajarsa a kan kyawawan ɗabi'u, kyakkyawar mu'amala, da neman yardar Allah, zai rayu cikin natsuwa ko da mutane sun yarda da shi ko ba su yarda ba.