@bahuzmedia: Kalli yadda Malam Abubakar Alƙali Salihu Zaria ya zauna cikin ƙasaita a lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kai ziyarar gaisuwa ga Alhazan Kaduna a masauƙinsu da ke Mina, ƙasar Saudiyya, yayin aikin Hajjin bana. Abin da ya ja hankalin mutane shi ne yadda malamin ya kasance cikin natsuwa da kwanciyar hankali, yayin da sauran mahalarta taron ke sauraron saƙon gwamnan. A ra’ayinku, shin wannan wata alama ce ta ƙasaita da matsayin malami, ko kuwa akwai wata fahimta daban? #bahuzmedia #fyp