@voice_of_sahaba: Shaykh Bin Uthman ya yi digiri na ɗaya da na biyu duka a B.U.K... Sannan ba a fannin addini ya yi su ba. Ya yi su ne ƙarkashin kimiyar siyasa da kuma ilimin tarihi. Wannan yake nuna cewa shek Bin Uthman duk karatunsa na Addini a Zaure ya kwankwaɗi ilimi da gaban malamai. Shekarun da ya yi wajen 30 yana da'awa shi ne ya ja hankalin University of Miami a ɓangaren sashin koyar da ilimin addini suka ga cancantar karrama shi da digirin digirgir saboda hidimarsa ta da'awa a ƙasashen duniya bakiɗaya. Shek Bin Uthman malamin duniya ne ba wai Afirka kawai ba. (International scholar) ne tun duniya na kwance. 🥰🥰🥰 Dr. Nebil Husayn shi ne shugaban sashin koyar da ilimin addini a University of Miami da suka yi wanann girmamawa. Alhamdu LILLAH. Mu a wajenmu shek Bin Uthman ya wuce haka, domin babu inda ba zai zauna a duniya ya karantar ba, ya iya yare kusan 7 kuma da ƙwarewa ba kame-kame ba; Larabci da Hausa da Turanci da Faransanci da sauransu... Allah ƙara wa shek lafiya da iyayenmu, ka sa aljanna ce makomarmu gabaɗaya. #