@mubeedabai: Mai Girma Sarkin Waƙar Kasar Hausa, Alhaji Dauda Kahutu Rarara, ya halarci taron addu’a na neman Allah Ya kawo mana zaman lafiya a Arewacin Najeriya da ƙasa baki ɗaya, wanda ƙungiyar Triple R Kannywood ta shirya a yau a Birnin Kano. Bayan kammala taron addu’ar, an gudanar da yanka tare da yin addu’o’i na musamman da nufin Allah Ya kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Arewacin ƙasarmu da Najeriya baki ɗaya. Allah Ya amsa addu’o’inmu, Ya tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasa baki ɗaya. Amin. 🤲🏽 Mubarak Dabai Mataimaki na Musamman ga Alhaji Dauda Kahutu Rarara