@basharsok3: Yadda mai girma ɗan takarar gwamnan jihar Sokoto a karkashin tutar jam'iyyar ADC HE. Hon. Manir Dan Iya FCNA (Walin Sokoto) ya halarci ɗaure–ɗauren auruka da gaishe–gaishen rasuwa a cikin garin Sokoto da wasu daga cikin kananan hukumomi a jihar Sokoto. Mai girma Walin Sokoto ya wakilce Sen. Aminu Waziri Tambuwal, CFR (Mutawallen Sokoto) a wasu wurare daban-daban inda ya samu rakiyar mutane daban-daban da suka haɗa da Shugaban jam'iyar ADC Hon. Abdullahi Maigwandu ɗan majalisar tarayya mai waƙiltar kananan hukumomin Binji da Silame Hon. Mani mai shinko Katami tsoffin kwamishinoni da tsoffin shuwagabannin kananan hukumomi yan siyasa malammai da ƴan takar kari daban-daban a jam'iyyar ADC a jihar Sokoto. Muna rokon Allah SWT ya basu zaman lafiya tareda zuri'a dayyiba, wadanda Allah ya yiwa cikawa Allah ya jikan su da gafara. Ameen –######### –Wali media aide