@mohbashow: Idan har da gaske kake yi, ga abubuwan da dole ne ka sa a ranka: 1. Jini Da Hawaye: Nasara ba ta zuwa da sauƙi ko da lissafin sa'a. Tana buƙatar sadaukarwa, rashin bacci, gumi, da hawayen ɓacin rai a ɓoye. Tana zuwa ne ga wanda ya ƙi bayar da gari koda ya fuskanci ƙalubale. 2. Shirya Cin Kasa: Ka daina tsammanin abubuwa za su tafi maka sumul babu cikas. Za ka faɗi, za ka yi asara, za ka ji kamar ka tsaya a wuri ɗaya. Wannan wani bangare ne na tafiyar, ba ƙarshenta ba. 3. Fara Daga Kasa: Duk wanda ka gani a saman bene, akwai lokacin da yake ƙasa. Kada ka ji kunyar fara ƙaramar sana'a ko aikin da mutane za su yi maka dariya a kansa. 4. Kashe Jiran Taimako: Kada ka tsaya jiran wani ya kawo maka jari ko 'yan uwa su riƙa hannunka. Fara takawa da abin da kake da shi a yanzu, koda kuwa kai kaɗai ne a kan hanyar. 5. Kasala Ƙabarin Buri Ne: Kasala da son jiki su ne suke haƙa ramin da ake binne manyan mafarkai. Tashi ka fuskanci wahalar neman halas ɗinka ba tare da tsoro ba. Rayuwa ba za ta taɓa tausaya maka ba saboda kana matashi ko kana da kyawawan mafarkai. Ka Tashi ka fuskanci zafin gumi a yau, domin ba za a yi maka jaje ba a gobe idan ka kasa. Allah yasa mudace #mohbashow ✍️#goviral
Moh Bashow
Region: NG
Friday 03 July 2026 12:36:29 GMT
Music
Download
Comments
Muhammad Yaro :
of course
2026-07-03 17:09:21
0
idrissafaical37 :
🥰🥰🥰
2026-07-03 20:18:23
0
To see more videos from user @mohbashow, please go to the Tikwm
homepage.