@saddamlabana0: Daga Gidan Marigayi Khadi Malami Bayan tsohuwar Tashar Mota Birnin Kebbi inda ake cigaba da Taaziyar Hajiya Aminatu ( Makuwara ) Al'ummar jihar Kebbi Musamman Yansiyasa da Yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati sun jajentawa Dan takarar Gwamnan Jihar kebbi Karkashin Jam’iyar ADC kuma gwamnan jihar Kebbi na gobe in Sha Allahu, Dr Abubakar Malami SAN bisa ga rasuwar mahaifiyar su marigayiya Hajiya Aminatu Makuwara, daya daga cikin matan marigayi Khadi Malami, wada Allah yayyima Rasuwa Jiya 04/07/2026.