@fauziyya_d_sulaiman: Update: Alhamdulillah, bayin Allah sun tarawa wadannan bayin Allah Naira Miliyan Daya Da Dubu Dari Takwas da sittin (1.860ml), da farko mun biya duka basukan da ake binsu, sannan muka siya musu kayan abinci, muka sai kayan solar panel da batiri da komai aka hada musu solar, aka bata sauran kudinta a hannunta, Allah ya sakawa wadanda suka taimaka da alkairi, Allah ya faranta muku duniya da lahira amin. IRIN ILLAR DA CIWON SIKILA(SICKLE CELL DISEASE) KE YIWA DAN ADAM Wannan matashin da aka dauka a hannu shekararsa 27, kuma tsahon wannan lokacin mahaifiyarsa ke yi masa komai, ko bahaya zai yi sai ta dora shi a fo, na biyun shekarunsa Goma sha Takwas shima sai mahaifiyarsa ta zaunar da shi ta tayar da shi, sai macen shekarunta Ashirin da Hudu, ba aure ba karatu, sai tabuwar Kwakwalwa da ciwon ya haddasa mata😭🙏. Wannan baiwar Allah ubangiji ya jarrabeta da yara uku masu ciwon sikila, wato duk irin dauriyarka idan kaga halin da baiwar Allah nan ke ciki da dawainiyar da ta ke yi da yaran sai ka tausaya mata, komai na ta ya kare, kusan shekaru ashirin da Takwas baiwar Allah tana fama da yarannan guda uku, biyu sai ta yi musu komai, ita kuma dayar da ta ke iya komai tana da matsalar kwakwalwa wato iyayan da ke da wadannan yaran suna shiga damuwa da wahala abun tausayi. Ku kalli dai halin da wannan baiwar Allah ta ke ciki, wahala da basuka sun dabaibayeta, wannan rayuwa ce mai cike da tashin hankali da rudani. Al'umma don girman Allah ku shiga lamarin baiwar Allah nan, musamman basukan da ke kanta don girman Allah🙏🙏🙏. Ga wanda Allah ya baiwa ikon shiga lamarin baiwar Allah nan za ku iya iya shiga🙏🙏. 0*1*09*2*9*93*75, Access, Creative Helping Needy Foundation. Allah ya ba ku ikon shiga lamarinsu, amin ya Allah🙏 NB: MASU SO SU YI AURE BAYAN AN SANAR DA SU ZA SU IYA HAIFAR YAYA MASU WANNAN CIWON, KU GA IRIN ABUN DA ZA KU IYA JEFA YAYAN DA ZA KU HAIFA A GABA, SUMA WADANNAN IYAYAN RASHIN SANI.
fauziyya d. Sulaiman
Region: NG
Sunday 05 July 2026 20:36:28 GMT
Music
Download
Comments
maman safiyya :
Allah yamuku sakamako da gidan aljannar firdausi Allah yadoraku akan makiyanku Allah yamuku jagoranci
2026-07-06 07:26:21
18
M I😎 :
Allah kabamu arzikin da zamu taimakawa mutane kabamu arzikin daba talauci bayanshi kabamu arziki Mai albarka 👍🥰
2026-07-12 09:03:02
12
شمحة🧕 :
gsky akwai mutanen Allah a duniyar nan🥺Allah ya Saka mu su da Alkairi
2026-07-10 07:03:13
6
aishaabba78 :
Aunty fauziyya ALLAH yayi miki tikuici da gidan Aljannah addu,ata dake a kullum, ALLAH yasa ki gama da duniya lfy Amin
2026-07-10 14:22:26
7
aunty bee :
kai Masha Allah wlh naji dadi sosai Allah yasaka da mafificin Alkhairi Allah yayi tukwaici da gidan aljannah
2026-07-06 14:24:14
6
mai-mota Glam home :
Allah Sarki Allah yai musu tsari daga sharrin barayi
2026-07-19 08:52:49
1
el rufai :
hajiya fauziya whl sai kin gama da duniya lafiya
2026-07-16 09:18:39
1
jamilaalasanzangi :
Allah sarki wanda yyi.hawaye yaddanmin like
2026-07-10 12:42:16
1
Secret Glam🥰🌹 :
Allah ya saka da alkhairi 🙏 Allah ya kawo mai daukar nauyin ciwon su a asibiti ameen 🙏🙏
2026-07-20 21:44:06
1
A’isha :
Alhamdulillah 😭😭
2026-07-05 21:22:25
1
maman safeeya :
ubangiji allah y biyaki da gidan aljannah,da ke d sauran al'ummar da su ka taimakausu
2026-07-11 20:26:50
1
mumfarha1 :
Alhmdlh Masha Allah🥰🥰🥰Allah yasa amizani😭
2026-07-07 04:45:21
2
Fatima Binta idris :
Allah ubangiji ya biya ku da aljanar fiddausi 🤲🤲
2026-07-07 21:10:34
1
@kakafatime :
aunty fauziya dan Allah dan annabi ki taimakeni da kudin jari 😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭ni marainiyace banida uwa banida uba 😭😭😭😭😭😭😭😭😭
2026-08-07 04:41:05
1
Abdou Akala :
allah yabiyaki ouwar marayou
2026-07-07 20:39:26
1
sunusi sunusi AA first bank 31 :
Allah yabiyaku.da.alkairi.anty.fauziya
2026-07-10 20:27:53
2
mama Amatanla :
Masha allahu🥰💯💯💯💯💯👍
2026-07-10 12:08:24
1
malam Ibrahim :
جزاكم الله خيرا
2026-07-05 20:44:43
1
Shemau Umar (multipurpose ) :
Allah yasaka da gidan aljanna
2026-07-05 20:59:19
1
@Danxila’s Lagos collections :
Ameen y hayyu y kayyum 🤲🤲🤲
2026-07-05 20:51:03
1
BINTU USMAN :
Allahumma barik Allahumma kudidna
2026-07-05 21:13:52
1
bint Aliyu :
mashaa Allah wato tun a duniya kk gane Yan aljanna anty fauziyya muna Miki kyakkyawan zato
2026-07-09 19:37:36
3
AMRISH CHICKEN :
ya allah ya baku lfy yabawa unty fauxiyya lada ameen
2026-07-09 22:19:18
1
maman nana :
Masha Allah Allah yasakamuku da alkaire
2026-07-05 20:42:51
2
To see more videos from user @fauziyya_d_sulaiman, please go to the Tikwm
homepage.