@marke.herbal.medicine: ALAMOMIN CUTAR KANJAMAU NA FARKO FARKO (HIV) 1. Zazzabi da yaki ci yaki cinyewa; idan ana jin hakan har makonni bayan shan magani, a je ayi tes na cutar kanjamau. 2. Ciwon makoshi, wanda ake kira sore throat, idan ya hadu da sauran alamu, a binciki lafiya. 3. Kurarraji a fata. 4. Gumin dare bayan mutum na cikin ni'ima 5. Kaluluwa. 6. Yawan ciwon jiki da gabobi. 7. Gajiya da raki, bayan ba'a yi aikin komai ba. 8. Barkewar zawo. 9. Yawan ciwon kai, maras dalili 10. Amai ko tashin zuciya. KARIN BAYANI: Saidai Kuma ganin wadannan signs din ba shine yake nuna cewa mutum Yana da ita ba, har sai anje asibiti anyi gwaji. Allah ya karee mu baki daya.🙏