@sardauna_shoot.ng: Bisa umarnin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, kuma daidai da manufofin Kano First Agenda, Babbar Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Ilimin Mata (SSA Women Education), Injiniya Yasmin Mukhtar, ta samu nasarar kammala Gangamin Wayar da Kan Dalibai Mata kan Muhimmancin Samun Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) da kuma Rajistarsa a manyan cibiyoyin ilimi guda uku na Jihar Kano. An fara gangamin ne a Federal College of Education (Technical), Bichi, daga nan aka ci gaba a Sa’adatu Rimi College of Education, sannan aka kammala a Federal College of Education, Kano, inda aka wayar da kan dubban ɗalibai mata kan muhimmancin kasancewa masu ruwa da tsaki a harkokin dimokuraɗiyya, amfani da haƙƙinsu na zaɓe, da kuma mallakar Katin Zaɓe na Dindindin (PVC). Wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin Gwamnatin Mai Girma Gwamna na ƙarfafa mata ta hanyar ilimi, shugabanci, da kuma ba su damar taka rawar gani wajen gina makomar Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya. Kano First!!! Ƙarfafa Mata!!! Gina Dimokuraɗiyya Mai Ƙarfi!!! #KanoFirst #KuriaGidaGida #WomenEducation #HerVoiceHerVote #PVCRegistration

Abba Is Working
Abba Is Working
Open In TikTok:
Region: NG
Tuesday 07 July 2026 19:02:26 GMT
1647
206
4
1

Music

Download

Comments

philosopher449
philosopher :
inshallah 🤲
2026-07-07 22:45:37
0
nasir.ibrahim195
Nasir Ibrahim :
falle daya ce insha allah
2026-07-07 23:58:50
0
user144465683090
ابكرمحمدادم :
🥰🥰🥰
2026-07-07 19:29:03
0
ameer.jr4
Ameer jr :
🙏🙏🙏
2026-07-07 22:50:57
0
To see more videos from user @sardauna_shoot.ng, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About