@kalaman_so_001: Na taɓa tunanin wanda nake matuƙar so ba zai taɓa zama dalilin hawayena ba… 💔 Na ba ki zuciyata ne saboda na yarda da ke, na ɗauke ki a matsayin wurin da zan samu natsuwa idan duniya ta gajiyar da ni. 🥺❤️🩹 Amma ban sani ba… hannun da nake tsammanin zai share min hawaye, shi ne zai sa su zubo. 😭💔 Har yanzu ina sonki… amma duk lokacin da na tuna abin da kika yi min, zuciyata tana tambayata: “Me yasa wanda ka fi so… shi ne ya fi sanin inda zai taɓa ka ka ji ciwo?” 💔🥀😭