@nasararadio98.5: Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya bayyana cewa ya taɓa ƙin biyan kuɗin fansa na Naira miliyan 300 lokacin da masu garkuwa da mutane suka sace 'yan'uwansa a shekarar 2019, yana mai cewa biyan kuɗin fansa na ƙara ƙarfafa masu aikata irin waɗannan laifuka. Jaridar punch ta rawaito Lawal ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin taron ARISE News da THISDAY, da aka gudanar a ɗakin taro Town Hall Conference dake Abuja. A cewarsa, lokacin da aka yi garkuwa da 'yan'uwansa, masu garkuwar sun nemi Naira miliyan 300 a matsayin kuɗin fansa, amma ya ce musu ba zai biya ko sisin kwabo ba, ko da kuwa za su kashe su. Gwamnan ya ce bayan shafe watanni uku a hannun masu garkuwar, an sako 'yan'uwan nasa ba tare da an biya ko kwabo ɗaya ba. Ya ƙara da cewa har yanzu matsayinsa bai sauya ba, yana mai jaddada cewa ba zai taɓa tattaunawa ko biyan kuɗin fansa ga masu laifi ba, domin hakan na ƙara musu ƙarfin gwiwar ci gaba da yin garkuwa da mutane. Lawal ya kuma sake nanata buƙatar kafa 'yansandan jihohi, yana mai cewa gwamnoni na fuskantar ƙalubalen ɗaukar alhakin tsaro alhali ba su da ikon bayar da umarni kai tsaye ga hukumomin tsaro.
Nasara Radio 98.5 FM
Region: NG
Thursday 09 July 2026 20:50:36 GMT
Music
Download
Comments
There are no more comments for this video.
To see more videos from user @nasararadio98.5, please go to the Tikwm
homepage.