@aleeyuu001: 📢 SANARWA GA IYAYE DA MASU KULA DA YARA Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu. Muna sanar da ku cewa, In shaa Allah, za mu fara sabon shirin karatu daga mako mai zuwa, kamar yadda aka saba bayan kammala hutu. A wannan karo, za a ba da damar yin rajista ne a cikin satin farko kawai ga duk masu sha’awar shiga wannan shiri. Don haka muna roƙon iyaye da su gaggauta yin rajistar ‘ya’yansu domin kada su rasa wannan dama. Bayan kammala satin farko, ba za a ƙara karɓar sabbin ɗalibai ba, sai a jira lokacin da za a sake buɗe rajista. Allah Ya ba mu ikon cin gajiyar wannan shiri, Ya sa ya zama alheri ga yaranmu. Ameen
Aliyu Muhammad Lawal
Region: US
Monday 20 July 2026 20:08:40 GMT
Music
Download
Comments
There are no more comments for this video.
To see more videos from user @aleeyuu001, please go to the Tikwm
homepage.