@dan_._gombe: ❤️🌹 Zuwa ga My Sweetheart Farin Cikina Masoyiyata Abar Ƙaunata 🌹❤️ Ke ce farin cikin da zuciyata take nema a kowace rana Idan na tuna da ke damuwata tana raguwa zuciyata kuma tana cika da natsuwa da farin ciki Ba zan taɓa mantawa da irin soyayya kulawa da ƙaunar da kika nuna min ba Kin zama wani ɓangare na rayuwata da ba zan iya rayuwa ba tare da shi Murmushinki yana haskaka ranata muryarki kuma tana sanya zuciyata ta yi farin ciki Ina godiya ga Allah da Ya kawo ki cikin rayuwata Duk ranar da na yi tare da ke tana zama ta musamman a gare ni Burina shi ne in ga kina farin ciki kina murmushi kuma kina samun duk abin da zuciyarki take buri Ki sani cewa kina da matsayi na musamman a zuciyata wanda babu wani da zai iya maye gurbinsa A yau gobe da har abada zan ci gaba da ƙaunarki da girmama ki Ina sonki My Sweetheart farin cikina masoyiyata abar ƙaunata Allah Ya kiyaye ki Ya kuma ƙara mana soyayya mai albarka❤️🥰🌹 #creatorsearchinsights #fypシ゚ #sweetheart #reletionship