@muhasa_92.3fm: Yadda Kotu a Kano ta yankewa Shu’aibu Abdulkadir hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin kashe wata matar aure mai suna Ruma Shu'aibu. Lamarin ya faru ne a ranar 6 ga watan Afrilun 2025, a unguwar Tsamiyar Duhuwa Farawa dake karamar hukumar Kumbotso Kano. Kotun ta samu Sha'aibu da laifin daure wuyan Ruma sannan ya yi amfani da wuka ya yankata.