@lbk4366: 🔴Wata sabuwa: shugaban ƙasar Nijar bai yadda Usmanu Danfodiyo j@hadi ya yi ba a ƙasar Hausa. A cikin jawabin da ya gabatar a yau a Jahar maradi da kuma ba da tarihin Gobir da Katsina da ya yi shugaban ya yi ya yi watsi da batun cewa: Usmanu danfodiyo Jihadi ya yi ba in da ya nuna lamarin ba haka bane. Inda ya kawo misalin hatta shi danfodiyo a nan daular Gobir ya ta so ya yi karatu da ilimi duk a ƙarƙashin daular ta Gobir inda yace ana kiransu "Arna" yace idan arna ne za a samu malamai da har shi Danfodiyo zai yi karatu a ƙarƙashin su? Daga ƙarshe Babban janar ya ba da asalin abinda ya faru, inda ya nuna rikici ne ya ya ta so tsakanin Daular Gobir da shi Danfodiyo wanda daga ƙarshe ya zama ya ayyana Jahadi kansu. Ma'ana dai Akwai siyasa da sha'anin mulki a wancan abin da abinda ake kira "jihadi" a yau. Menene fahimtar ku kan wannan batu? Abouzeidou Barmini Mayaou #Hausa #nigeria #hausazallah #Niger