@trtafrikaha: Iran ta saki wani bidiyo da ba kasafai ake ganin irinsa ba wanda ya nuna Jagoran Addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei da ransa, bayan wasu rahotanni sun yi iƙirarin cewa hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai sun jikkata shi sosai tare da sauya kamanninsa. Iran a ranar Lahadi ta bayyana cewa Mojtaba ya gana da Shugaban Iran Masoud Pezeshkian, wanda ke fara shekara ta uku a matsayin shugaban ƙasar. An zaɓi Mojtaba a matsayin Jagoran Ƙoli na Iran a farkon watan Maris, bayan an kashe mahaifinsa, Ali Khamenei, a wani harin sama da Amurka da Isra’ila suka kai a ranar 28 ga Fabrairu. Tun bayan zaɓensa, ba a sake ganinsa a bainar jama’a ba. Kamannin Khamenei sun “sauya sosai” sakamakon harin da aka kai a harabar gidan Jagoran Addinin ƙasar da ke tsakiyar Tehran, sannan “ya samu mummunan rauni a ƙafa ɗaya ko kuma ƙafafunsa biyu”, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito a watan Afrilu. A watan Yuli, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Mojtaba Khamenei yana “dab da mutuwa” saboda raunukan da ya samu, a yayin wata hira da gidan talbijin na Fox News.

TRT Afrika Hausa
TRT Afrika Hausa
Open In TikTok:
Region: NG
Tuesday 11 August 2026 09:01:58 GMT
8731
826
6
14

Music

Download

Comments

younousssalah
🍀 ابن صلاح/يونس عمر :
Masha Allah Allah ya kare shi
2026-08-11 11:38:12
0
itx_excort
Bara'u Rabi'u :
🥰🥰🥰
2026-08-11 10:20:18
0
man575400
man :
😳😳😳
2026-08-11 10:10:14
0
mahamadousalaabdou
Abdoul89 Dan Tahoua :
😂😂😂
2026-08-11 09:08:48
0
alhaji_yusif
Yusuf abdullahi :
🥰🥰🥰
2026-08-11 09:08:47
0
patronba83
patronba# :
🥰🥰🥰
2026-08-11 10:26:11
0
To see more videos from user @trtafrikaha, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About