@watnewshausa: Tsohuwar ‘yar majalisar wakilan Amurka, Marjorie Taylor Greene, ta yi iƙirarin cewa ana tattauna yiwuwar amfani da makaman nukiliya kan Iran a wasu tarukan dabarun yaƙi na Amurka. "Eh, gaskiya ne. Ba hasashe nake yi ba, na sani. Kuma wannan mummunan aiki ne." inji Greene. Sai dai ba ta gabatar da wata hujja da ke tabbatar da iƙirarinta ba, kuma babu wata sanarwa a hukumance daga Fadar White House ko Pentagon da ta tabbatar da cewa ana tattauna amfani da makaman nukiliya kan Iran. Shin me za ku ce game da wannan?