@d3tv247: Matukar kana kan mulki, kuma kana son magance kowani matsala, toh sai ka saukar da kanka kasa ka dawo daidai da mutane. Da yardan Allah nine zan kawo karshen Mulki APC a jihar Neja. Ba aiki bane ba'a yi a jihar Neja, Wanda ya shafi talakawa ne Ba'a dauko hanya ba ko har yanzu. Alumman jihar Neja Sunyi kyakkyawan zato akan mulkin Mai Girma gwamnan jihar Neja Umaru Mohammed Bago kasancewarsa ya karbi mulki a matsayin Matashi. Wadannan ZAFAFAN Zantukan Alhaji Yahaya Mohammed dan takaran kujeran Gwamnan Jihar Neja karkashin Jam'iyar NDC kenan acikin shirin WAKILCI wanda zaizo maku gobe da misalin karfe 8 na dare.