@trtafrikaha: Iran na duba yiwuwar kai gagarumin hari kan kadarorin sojojin Amurka a Turai idan Shugaba Donald Trump ya ƙara ƙaimi a yaƙin da suke gwabzawa, yayin da Tehran ke neman faɗaɗa rikicin fiye da Gabas ta Tsakiya, a cewar Jaridar Financial Times. Da take ambato wasu mutane biyu da ke kusa da gwamnatin Tehran, jaridar ta Birtaniya ta ce sojojin Iran sun tabbatar da yiwuwar kai hari kan cibiyoyin Amurka a ƙasashen kudu maso gabashin Turai, ciki har da Bulgaria, wadda a watan da ya gabata ta amince Amurka ta yi amfani da sansanin sojin samanta na Bezmer don kai hari Iran. Kudancin Cyprus da ke ƙarƙashin ikon Girka, inda wani jirgi maras matuƙi ya faɗa kan sansanin sojin saman Birtaniya a watan Maris, na daga cikin waɗanda za a iya kai wa hari idan Amurka ta sake kai hari Iran, a cewar ɗaya daga cikin majiyoyin. Wata majiya ta shaida wa jaridar Financial Times cewa Tehran na shirin faɗaɗa rikicin idan Trump ya aiwatar da barazanar da ya yi a baya bayan nan ta kai hari kan kayayyakin more rayuwa na Iran. "Idan Amurka ta yi nisa sosai, Iran za ta kare kanta a kowane yanayi, ta wuce yankin ta kuma kai hari kan Turai ma," in ji majiyar. Rahoton ya zo ne yayin da tattaunawa kan sake buɗe Mashigar ruwa ta Hormuz ta tsaya cak kuma hasashen sake buɗe mashigar ruwan daga Tehran da Washington ya ragu. Trump a ranar Talata ya bayyana cewa babu "wata tattaunawa ko ganawa da ake yi, ko aka tsara yi" da Tehran. Jami'an sojin Iran sun yi gargaɗin cewa duk wani sansanin soja da ake amfani da shi don kai hare-hare kan yankin Iran za a iya ɗaukar sa a matsayin wajen kai hari. Rundunar sojojin Iran ta yi nazari daban-daban kan yiwuwar kai hari kan wayoyin sadarwa na ƙarƙashin teku a Mashigar Hormuz idan aka ƙara kai mata hari.

TRT Afrika Hausa
TRT Afrika Hausa
Open In TikTok:
Region: NG
Wednesday 19 August 2026 13:22:26 GMT
10961
1087
17
4

Music

Download

Comments

sha___ban
S H A B A N :
Allah yasa
2026-08-19 15:42:00
1
bolaahmad20
Ahmad khan 🇳🇬💖🇸🇦🙏 :
Ira is power 🥰
2026-08-19 16:35:51
1
jameelfashiondesigner0
j. man :
3th world war is loading 😳😳
2026-08-19 17:54:53
2
abdulaye85
Sʜᴀᴍᴀ_ Uɴᴜ 🄲🅸🌴 :
Allah ya sa
2026-08-19 17:28:18
1
maharaz.bouzai.813
محـراذالبـوازيــــــىٰ🌹 :
2026-08-19 21:11:57
0
mustafasani967
mustafasani967 :
good
2026-08-19 23:03:08
0
salam.mahamat8
Salam Mahamat :
macha allha
2026-08-19 19:37:44
0
ashiruak11
Ashir ak :
Masha Allah
2026-08-19 17:35:33
1
fatimaaligoni2
Fatima ali goni :
Iran 🇮🇷 💪💪💪
2026-08-19 20:22:57
0
abbahassan003
ABBA :
Allah ya ba mai rabo sa'a ya taimaki musulunci da musulumai
2026-08-19 16:15:36
2
m.nazz003
Muhammad Nazifi Ibrahim :
ohhh new escalation 😳 Allah ya bawa Iran 🇳🇬🇮🇷 nasara
2026-08-19 15:52:45
1
ahmadismail9691
Ahmad Ismail :
Wllh kada kukai harinnan saboda wllh komai na’iya faruwa 👏
2026-08-19 19:20:45
0
abdallahgmb.227
Abdallah GMB :
Iran Gagara badau Masha Allah 😂
2026-08-19 18:27:00
0
0163142315ml
AA Lawali :
🥰🥰🥰
2026-08-19 17:59:32
0
mamantadji.zilede
mamantadji Ziledeini :
🥰🥰🥰
2026-08-19 19:32:18
0
official__sunusi__
S__gama🌹♥️🌹 :
🥰🥰🥰
2026-08-19 14:58:42
0
salam.mahamat8
Salam Mahamat :
🥰🥰🥰🥰😂😂😂
2026-08-19 19:37:53
0
To see more videos from user @trtafrikaha, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About