@trueloves63: 🤔😍🤔 Karkayi skipping wannan text indai kasan budurwarka bata kula dakai yadda yakamata Aslm baby barkanki da warhaka fatan kina lpy, baby Ruhina, kwata-kwata zuciyata ba za ta iya jure ganin wannan tazarar da ke ƙara nisa a tsakaninmu ba. Ke ce farin cikina, kuma a duk lokacin da na ji kika rage ba ni kulawa yadda kika saba, duk wani farin ciki na rayuwata tsayawa yake yi. Muryarki, saƙonninki, da maida hankalinki a gare ni su ne ke ba ni ƙwarin gwiwa da faranta mini rai a kullum. Shirunki yana sanya ni cikin tunani da fargabar ko na yi wani kure da ban sani ba. Don Allah masoyiyata, ki dawo mini da wannan kyakkyawar kulawar da kuma daɗaɗan kalaman da ke ƙara sanya mini natsuwa. Zuciyata tana matukar kewarki, kuma babu wata da za ta iya maimaye matsayinki a tare da ni. 💖🌹
Aliyu Bashir
Region: NG
Wednesday 19 August 2026 18:14:29 GMT
Music
Download
Comments
💫Official Emkay...🦅 :
Hmm some people don’t realize our worth until it’s too late.💔
2026-08-19 23:24:30
0
To see more videos from user @trueloves63, please go to the Tikwm
homepage.