@trtafrikaha: Adadin waɗanda suka mutu sakamakon zaftarewar ƙasa a mahaƙar ma'adinan zinari a yammacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya kai sama da 100, in ji wani jami'in Red Cross da ke cikin masu ayyukan agaji kuma wani jami'in yankin ya ce a ranar Laraba. Wajen haƙar ma'adinan zinarin ba bisa ƙa'ida ba ya rufta a safiyar Talata a ƙauyen Zamboye, a yankin Nana-Mambere, kusa da kan iyaka da Kamaru. Martin Ziguele, Shugaban Ƙungiyar 'Yantar da Jama'ar Tsakiyar Afirka, ya ce "gwamnati ce ke da alhakin faruwar waɗannan bala'o'i". Madugun 'yan hamayya na Kamaru Maurice Kamto ya ce hatsarin ya bayyana "rashin tausayin waɗanda suke samun kuɗi sakamakon gallaza wa masu aikin haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba". "Ba su nuna damuwa ko kaɗan game da yanayin da 'yanƙasa, waɗanda talauci ya tilasta musu yin aiki a wuraren haƙar ma'adinai marasa tsari, ba tare da matakan kariya ba," in ji Kamto, babban mai sukar shugaban Kamaru Paul Biya wanda ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2018.

TRT Afrika Hausa
TRT Afrika Hausa
Open In TikTok:
Region: NG
Thursday 20 August 2026 15:42:44 GMT
6067
352
3
2

Music

Download

Comments

amb_nababaru
Amb_nababaru :
Allah kasamu a Aljannah
2026-08-20 16:05:19
1
lamine.0009
Lamine 0009 :
ya Allah 🤲
2026-08-25 06:07:37
0
To see more videos from user @trtafrikaha, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About