@elfaruq02: Hajiya Naja’atu Muhammad ta bawa @Professor Isa Ali Pantami hakuri, kan kalamai marassa dadi da tayi a watannin baya. A daren jiya Asabar Hajiya Naja’atu Muhammad ta tura tawaga karkashin jagorancin Sarkin Hafizan kasar Hausa, Gwani Yusuf Hamza, shugaban majalisar Hafizan Al-Qur’ani ta kasa baki daya, suka ziyarci wasu daga cikin wakilan Professor Isa Ali Pantami da suka hada da Alhaji Abubakar Ahmad Walama (Sarkin Malaman Gombe), Professor Muhammad Bello tsohon shugaban hukumar Galaxy Backbone, Alhaji Hussaini (Dan Amar Din Gombe) da sauran Dattawa da matasa. Wakilan tawagar cikin girmamawa da tawali’u sunce sun kawo ziyara ne domin isar da sakon neman afuwa da sulhu ga Professor Isa Ali Pantami, bisa wasu kalamai marassa dadi da Hajiya Naja’atu Muhammad tayi watannin baya a gidan TV na Ali akan Professor Isa Ali Pantami. Wakilan sun gabatar da jawabai masu muhimmanci da jan hankali na neman yafiya kan abunda ya faru. Suma daga bangaren wakilan Professor Isa Ali Pantami sun yi tsokaci bisa jajircewar Hajiya Naja’atu na gane cewa tayi kuskure na maganganun da ta fada tare da bada hakuri.

El-Faruq
El-Faruq
Open In TikTok:
Region: NG
Sunday 23 August 2026 08:33:58 GMT
810
51
0
2

Music

Download

Comments

There are no more comments for this video.
To see more videos from user @elfaruq02, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About