Lamido Idu👑🇦🇺✅ :
Hausa ❤️Ina son ki ne domin in aure ki, ba wai don kawai in yi soyayya da ke ba. Idan maganar soyayya ce kawai, akwai mata masu kyau da yawa a duniya. Amma ke kaɗai ce nake gani a matsayin wadda ta fi dacewa da zuciyata. Ke kaɗai ce kika cancanta in kira ta sarauniya ta, ke kaɗai ce kika cancanta in mai da ke gimbiya a wannan zuciyar tawa. ❤️👑
Ke kaɗai ce nake so in gina rayuwa da ke, in riƙe hannunki, in kasance tare da ke, kuma in nuna miki cewa ke ce zaɓin zuciyata. A wajen kyau da kwalliya, ohhh Allah! Kina yi wa kaya kyau, kina yi wa ado kyau, kuma duk abin da kika sa yana ƙara nuna irin bambancin da ke da shi. Ko a wane fanni, ke ta dabam ce. ❤️🌹
Ba wai ina kallon kyawunki kaɗai ba ne; ina son ke saboda irin mutumin da nake ganin kina da shi a cikin zuciyarki. A gare ni, ke ba mace ce kawai ba—ke ce wadda nake so ta zama sarauniyar rayuwata. ❤️👑
English ❤️I love you because I want to marry you, not simply because I want to be in love with you. If it were only about love and beauty, there are many beautiful women in the world. But you are the only woman my heart truly sees as the one who belongs beside me. You are the only one I want to call my queen, and the only one I want to make my princess in this heart of mine. ❤️👑
You are the one I want to build my life with, hold your hand, stand beside you, and show you every day that you are the choice my heart has made. And when it comes to your beauty and the way you dress—oh my God! You make clothes look beautiful, you make every outfit look elegant, and no matter what you wear, you have a way of making it special. In every way, you are different and truly one of a kind. ❤️🌹
I don't love you only because of your beauty. I love you for who you are, for what you mean to my heart, and because you are the woman I want to make my queen and share my life with. ❤️👑
2026-09-02 02:10:54