@jagumaihala: TUNA BAYA: FURUCIN MARIGAYI SARKIN KANI ADO BAYERO KAN GINA COCI A BUK. “Ko Jonathan bai isa ya gina Coci a BUK ba” Zaman Babbar Kotun Shari’a (Federal High Court) da ke babban birnin tarayya Abuja, a kan ƙarar da Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa (CAN) ta kai Masarautar Kano, saboda Mai Martaba Sarkin Kano, Alh. Dr. Ado Bayero, ya sa an rushe wata Coci da ake ginawa a cikin tsohuwar Jami’ar Bayero Kano (BUK). A zaman kotun da aka yi a ranar Litinin, 3 February 2014, kwanaki 123 kafin rasuwarsa (Ado Bayero 06 June 2014), kotu ta nemi Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero, Prof. Rasheed, da wakilin Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa, da kuma Mai Martaba Sarkin Kano, da su bayyana a gabanta, a zaman kotun. An ga Prof. Rasheed da Mataimakin Shugaban CAN sun mike tare da Lauyoyinsu, amma ba a ga Mai Martaba Sarki ba. Daga nan sai jagoran Alkalan kotun, Justice Alakola Nweri, ya ce, da yake muna da sauran mintuna 10 kafin fara shari’ar, za mu jira zuwan Mai Martaba Sarkin kafin waɗannan mintocin. Daga nan sai Justice ya dubi Prof. Rasheed ya ce, a baya Kotu ta ba ku umarnin Gina Coci a Jami’ar Bayero, ko kun bi umarnin kotu? Prof. Rasheed ya ce, ƙwarai kuwa mun bi umarnin Kotu, don sai da ginin Cocin ya kai linta, sannan Mai Martaba Sarkin Kano ya ba mu umarnin tsayar da aikin, daga baya kuma sai ga Mai Girma Galadiman Kano, Alh. Tijjani Hashim, ya jagoranci Rushe ginin gaba ɗaya. Justice ya ce, kuna nufin kenan kun yi watsi da umarnin kotu kun bi na Sarki? Prof. Rasheed ya ce, ƙwarai kuwa, saboda Sarki Ubanmu ne, kuma shi ne Sarki mai daraja ta ɗaya a ƙasar nan bayan Sarkin Musulmi, saboda haka, ba za mu iya ƙin yi masa biyayya ba. Daga nan sai Justice ya umarci Prof. Rasheed da ya zauna. Justice ya ce da wakilin CAN, ka ji abin da ya faɗa, kana da abin cewa? Sai ya ce, Eh, wakilin CAN ya ce, gaskiya ne hukumar Makarantar Jami’ar Bayero ta fara gina Cocin, aka hana su, saboda haka muke roƙon wannan kotu da ta hukunta Sarkin Kano bisa shiga hurumin da ba nasa ba. Daga nan shi ma aka ce ya zauna. Sannan kotu ta nemi Sarki da ya bayyana a gabanta. Ana haka sai ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, Dr. Anyim Payios Anyim, ya bayyana a gaban kotun. An ga Alkalan kotun sun mike tsaye domin girmamawa ga Dr. Anyim. Daga nan Dr. Anyim ya ce, ya Mai Shari’a, ni ne wakilin Mai Martaba Sarkin Kano, Alh. Dr. Ado Bayero, ya umarce ni da na wakilce shi a wannan kotu domin amsa kira. Justice ya ce, kana nufin kana tsaye a nan a matsayin Mai Martaba Sarki kenan? Dr. Anyim ya ce, ƙwarai kuwa, kuma duk abin da zan faɗa ba ni na faɗa ba, His Royal Highness ne ya faɗa. Justice ya ce, muna jinka. Dr. Anyim ya ce, Sarki ya ce na sanar da wannan Kotu, shi ya sa aka rushe Cocin, ba don komai ba sai don ba sa buƙatar ganin Cocin a Jami’ar. Sannan ya ce, na gaya wa wannan kotu mai daraja cewa, idan za a gina Coci sau 10 a Jami’ar, to kuwa zai sa a rushe ta sau 10. Sannan Galadiman Kano, Alh. Tijjani Hasheem, ya ce na gaya wa wannan Kotu, ko Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan bai isa ya gina Coci a harabar Jami’ar Bayero ba, ba tare da yardar Mai Martaba Sarki ba. Dr. Anyim ya ci gaba da cewa, wannan shi ne saƙon da Mai Martaba Sarkin Kano da Mai Girma Galadiman Kano suka turo ni domin na sanar wa wannan kotu. Na gode. Daga nan, an ga Alkalan Kotun suna tattaunawa a tsakaninsu, kafin daga bisani aka ga Babbansu ya ɗaga waya yana magana. Daga nan sai Alkalin ya ce, to, duk mun ji. Ba ya nan ku, don haka, wannan kotu tana kira ga Shugaban ƙasa da ya duba wannan lamari. Idan ya ga da yiwuwar gina Cocin, to ya ba da umarnin ginin, idan kuma ya ga ba sai an gina ba, to shikenan. Daga ƙarshe, Kotu ta sallami wannan ƙara, kuma tare da yi wa Mai Martaba Sarkin Kano fatan alkhairi da fatan Allah ya ƙara masa lafiya da adalci. Sai dai bayan gama wannan shari’a, Mai Girma Galadiman Kano ya bayar da sanarwar cewa Babbar Mai Shari’a ta ƙasa, Ju Kano, Alh. Dr. Ado Bayero CFR. LLD. JP. Allah Ya Jaddada Rahama Ga Sarki Ado Da Dukkan Musulmai, Allah Ya Kai Masa Ladansa Na Yiwa Addinin Musulunci Hidima. Amin, summa amin.

JAGU MAI HALA 😍❤️
JAGU MAI HALA 😍❤️
Open In TikTok:
Region: NG
Saturday 29 August 2026 00:07:34 GMT
12379
645
27
21

Music

Download

Comments

ummansu85
aminabashir881 :
Ameen ya rabbi
2026-08-29 14:02:26
0
ceo.qlty
QUALITY SOLAR ENERGY :
Allah ya ji kansa da rahama amin yaa rabbi yaa huyyu yaa quyyum
2026-08-29 12:45:34
1
sanusi.ahmad.abba
Sanusi Ahmad abba :
allah yajadda rahma agareku ju9g
2026-08-29 10:48:16
1
faruksanda
farouq umar :
Allah ya jikan Shi Da rahama 🙏
2026-08-29 11:22:41
1
aa.sale1
aa sale :
ya rabbi yaji qan ado bayaro
2026-08-29 10:58:37
1
gandawa04city
Dayyab Mohammed :
Allah sa mudace
2026-08-29 14:23:14
0
aminu.ismaila01
Aminu Ismaila :
wallahi wannan labarin karya
2026-08-29 12:14:45
1
real.sadeeq.024
real sadeeq :
Allah yajikansa
2026-08-29 13:39:25
0
abk3952
Abk :
Hmmmm Allah ji kan mazan gaske
2026-08-29 14:05:08
1
090habipte
Armour557_🇳🇬 :
Allah ya jiqan shi da rahma
2026-08-29 13:48:05
0
daniel.ajik
Daniel Ajik :
Aduniya kenan
2026-08-29 12:32:31
0
baban.yara154
Baban Yara :
Maza maganin maza
2026-08-29 11:05:06
0
doctor.yarima
doctor yarima :
mazan jiya 💯💯
2026-08-29 09:58:00
0
abubakarmohammedyabo
abubakarMohammedyabo :
Allah yajikan sa da rahama
2026-08-29 11:10:03
0
sanik.lawan
saniklawan :
Allah ya jikansa da rahamah
2026-08-29 11:25:41
0
aymangold32
Ayman_Gold_Jewelry :
Allah Ubangiji yajikan mai martaba
2026-08-29 13:11:07
0
musab_ibraheem
musab Ibrahim khaleel :
Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum 😭 🙏
2026-08-29 03:23:39
0
sanusiadamu112
SA Rabah :
mazan jiya Allah swt ya yi maka rahama .
2026-08-29 11:53:08
0
anas.d.inuwa
Anas d Inuwa :
Allah ya jaddada rahama
2026-08-29 14:43:53
0
and_drew2
and_drew2 :
Meyasa bai kori christians a jahar Kano ba
2026-08-29 13:14:35
0
umarjafarnasaru
umarjafar863 :
Allah yaqaramasa kusanci da annabin. Tsira
2026-08-29 10:01:54
0
captainbuhari22kano
Buhari captain, :
Allah ubangiji kajikansu kamusu rahama sabida rahamarka dajinkanka.
2026-08-29 09:16:00
0
alaaji_waya
Alaajiwaya :
Ay kuwa yanxu tinda masaurata biyu ake da ita sai su dawo suyi churchin su
2026-08-29 11:54:28
0
capitalgausi
capitalgausi :
Allahu Akbar Maza abun labari,Allah ya qara ragamar Rahma a gare ka Dan mutuncin Annabi Muhammadu saw
2026-08-29 13:32:29
0
To see more videos from user @jagumaihala, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About