@pantami_supporter1: Daga shekarar 2019 zuwa yanzu 2026, Gwamnatin jihar Gombe tace ta kashe kimanin Naira biliyan 138 domin samar da ruwan sha a jihar Gombe, amma har yau ruwa na bawa al'ummar jihar Gombe birni da karkara wahala, kamar yadda IG Wala ya bayyana. Shin sai yaushe za'a fara samun ruwan fanfo a Gombe?