@arewa_presenter: BARAZANAR TSARO: Israila ta Dauki Matakin Gaggawa Saboda Iran. Tsaro ya ƙara tsananta tsakanin Iran da Isra’ila! 🇮🇷🇮🇱 Shin Bet ta tabbatar da cewa an dawo da Yair Netanyahu, ɗan Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, daga Miami zuwa Isra’ila cikin gaggawa bayan gano wata babbar barazana ga rayuwarsa. Netanyahu ya riga ya bayyana cewa Iran ta yi ƙoƙarin kashe ɗaya daga cikin ‘ya’yansa, yayin da rahotanni suka danganta barazanar da wani shirin Iran a Florida. Amma Shin Bet ba ta bayyana cikakken bayanin wanda ke bayan barazanar ba. Me wannan ke nufi ga sabon rikicin Iran da Isra’ila? #Iran #Israel #YairNetanyahu #BenjaminNetanyahu #ShinBet