@amanar.samira: Mafi yawan mutane a yau suna yin sallah, amma ba kowa ne ya iya dukkan karatun sallah daidai ba. 🤲🏽🕌 Saboda haka, na ga ya dace in saka karatun Tahiyya a rubuce, domin wanda bai haddace ta ba ya samu damar karantawa ya koya, musamman waɗanda suke son gyara sallarsu. Ba wai don a dogara da rubutu har abada ba ne, sai dai domin taimakawa wajen koyo da haddacewa. Allah Ya sa mu dace, Ya karɓi sallolinmu, Ya koya mana abin da ba mu sani ba. 🤲🏽❤️ Amanar Samira ✍️