Muhammed :
Wacce Allah Ya azurta da miji nagari, mai kyautatawa iyayensa, mai hannu a bude, mai kyawawan halaye, mai sauƙin mu’amala, to ta ji tsoron Allah, ta girmama shi, ta tausaya masa, kuma kada ta butulce masa.
Wanda Allah Ya azurta da mace tagari, wacce ta tattara siffofin mace Musulma, to ya tausaya mata, ya kyautata mata, ya yafe mata kurakurai, ya kuma yi afuwa ga gazawarta.🙏
2026-09-21 12:24:28