@abba_bloger: Dr. Usman Muhammad Abdulhamid (Presido), Shugaban Kano First Intellectual Progressive Movement #(KFIPM), ya yi tayin ₦1m ga duk wanda zai iya ba da amsoshin wasu tambayoyi biyu. Ya kalubalanci ’yan Najeriya da su bayyana fa’ida guda ɗaya da talakawa suka samu sakamakon cire tallafin man fetur, sannan su kuma nuna wani aiki na ₦10bn a Jihar Kano da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ƙaddamar tare da kammala shi gaba ɗaya. Ya kuma kalubalanci magoya bayan gwamnatin #Tinubu da su bayyana dalili guda ɗaya da ya sa ’yan Arewa ya kamata su sake mara wa Tinubu baya a #zaɓen2027, yana mai cewa ’yan Najeriya na ƙara wayewa a harkokin siyasa kuma ba za a ci gaba da ɗaukar su da wasa ba. #kano #