@abdoulsheh: Mai Girma Gwamna Dr. Nasir Idris, Kauran Gwandu, ya zagaya aikin gina gidaje da ake yi a Garin Zauro, Kaura Housing Estate, domin duba yadda aikin ke gudana. Aikin ya kunshi gina gidaje 250, wanda zai taimaka wajen samar da ingantattun gidaje tare da inganta rayuwar al’ummar Jihar Kebbi. Mai Girma Gwamna ya ci gaba da nuna kulawa da jajircewa wajen tabbatar da cewa ayyukan raya ƙasa sun kammala cikin inganci, tare da samar da alfanu ga al’umma. Kaura Housing Estate — another milestone for a better Kebbi. 🏠💚