classichomeinteriors :
“Self-defence ne” ba ya nufin an gama magana.
Wannan ba adalci ba ne. Idan har abin da ya faru ya kai ga rasa ran mutum, ya kamata a yi bincike na gaskiya, a saurari waɗanda abin ya shafa, sannan a ɗauki matakin da ya dace.
Mutanen Gandun Albasa, Kano ma suna da hakkin samun tsaro, adalci da kariya. Their lives matter too. Ba za a iya yin sakaci da rayuwar mutane sannan a ce kawai “self-defence ne” a rufe maganar ba.
Gwamna yana mulkar mutane ne domin ya kare rayuwarsu da mutuncinsu, not to ignore the people he governs. Idan jami’i ya kasa fahimtar darajar rayuwar al’ummar da yake wakilta, to ya kamata a binciki lamarin, kuma idan an tabbatar da rashin cancanta ko wuce gona da iri, he should be held accountable and, where appropriate, removed from office.
Gandun Albasa na neman justice, ba son zuciya ba. Rayuwar kowa tana da daraja, kuma adalci ya kamata ya zama ɗaya ga kowa.
2026-09-10 13:54:08