@arewatracks: Fitaccen mawaƙin nan, Ado Gwanja, ya fito ya wanke kansa tare da gargaɗi mai zafi ga masu ci gaba da yaɗa jita-jitar cewa har yanzu yana kwance a asibiti yana jinya. A wani bayani da ya wallafa, Gwanja ya tabbatar da cewa tabbas ya yi rashin lafiya domin kuwa "cuta ba abin kunya ba ce," amma fa tun fiye da watanni biyu da suka gabata ya warke kuma ya baro asibiti! Mawaƙin ya nuna mamakinsa kan masu yaɗa labaran ƙarya, inda ya bayyana cewa ko hoto ɗaya bai bari an ɗauke shi ba lokacin yana jinya. Sannan ya ƙi bayyana irin cutar da ta kama shi, yana mai cewa hakan sirri ne tsakaninsa da mahaliccinsa da ya jarrabe shi. Don tabbatar wa da masoyansa cewa ya dawo bakin aiki, Ado Gwanja ya tuna musu cewa har sabuwar waƙa ya saki mai suna "Tabare" a kwanakin nan. Ya kuma buƙaci gidajen jaridu da masu wallafa labarai su riƙa bincike kafin su yaɗa labari. Me zaku ce game da wannan kalami na Ado Gwanja, musamman ga masu yaɗa labaran ƙarya? 👇 #adogwanja #arewatracks #foryou #arewa__tiktok #kannywood
Arewa Tracks
Region: NG
Friday 11 September 2026 05:03:08 GMT
Music
Download
Comments
Abu khausar ❤️ :
Allah sarki gwanja wllh kafi inyass amfani a Nigeria.
2026-09-12 10:55:26
32
Alasan Watara :
Patan alkairi [Heartwarming]
2026-09-12 20:54:31
0
BASHAR ALI GUSAU :
Rashin aure ne ke damun shi
2026-09-11 14:57:28
5
Abdullahi Aminu damfo kura :
fatan nasara in sha allahu abokina
2026-09-14 11:00:53
1
Basiru Abdullahi :
Karigasu Kace Allah Gwanja Fatan Alkhairi
2026-09-11 16:38:05
4
Bashari Ahmad :
Masha Allah Allah ya qara lafiya
2026-09-14 09:20:05
1
Khamal Ibrahim Galadima :
gaskiya gwanja duniya nw
2026-09-14 08:38:53
1
Mami ❤️🩹 :
Allah Yasa Yazama Kaffara Agareshi
2026-09-13 08:31:38
4
Harunabello42 :
gaskiyane gwanja mungodiya
2026-09-13 06:21:42
2
, :
kuma wallahi hkn kuma xata bare da yadda allah
2026-09-11 13:47:06
5
Hafsat ado :
masha Allah Allah yakara lpy Waka tayi dadi
2026-09-12 23:01:10
3
One billion dollars :
one love bro
2026-09-12 08:26:20
3
Bishir adamu danja kauranfawa :
allah sarki allah ya Kara lfy da nisan kwana 🙏
2026-09-12 18:57:28
3
sagiru dauda :
in Allah yayarda sai ta bare
2026-09-12 18:42:52
2
Kawu Juji Hardawa :
Masha Allah
Allah yakara lafiya da nisan kwana
2026-09-11 21:47:48
2
musahabibu :
masha allah
2026-09-11 07:55:04
3
BAHAGO ⭐⭐⭐ :
✌️✌️✌️✌️✌️✌️✌️✌️OK
2026-09-11 18:53:15
1
4k :
nice 👍
2026-09-11 22:17:31
1
zainab :
Allah ya karamaka lfy
2026-09-11 20:28:37
1
ibrahim-D2ta :
fatan alkhairi
2026-09-12 09:01:21
1
hakim2 :
Allah ykra basira
2026-09-11 23:38:24
1
@gighali ibrhim :
wallahi naji na kara kaunarka
2026-09-11 17:57:02
3
Raash Kabo :
Allah ya sakama da alkhire ado 🤲💯👍
2026-09-11 17:28:21
4
To see more videos from user @arewatracks, please go to the Tikwm
homepage.