@a.mquotes1: 🦋BARKA DA SAFIYA 🦋 ❤️🔥 Wataƙila Wannan Shi Ne Saƙona Na Ƙarshe... Na daɗe ina tunanin ko ya kamata in tura miki wannan saƙon. Amma zuciyata ta gaya min cewa wani lokaci mutum yana bukatar ya faɗi gaskiyarsa kafin ya yi shiru. Ban taɓa nadamar sonki ba. Ko da soyayyar ta kawo min hawaye, zan ci gaba da ɗaukar lokacin da muka yi tare a matsayin wani abu mai daraja a rayuwata. ❤️Amma yanzu na fahimci cewa ba kowane mutum da muke so ne aka halicce shi domin ya kasance tare da mu har ƙarshen rayuwa ba. Saboda haka, ba zan riƙe ki da ƙarfi ba. If letting you go is what gives you peace, then I will let you go. 🥺 Ki yi rayuwarki cikin farin ciki. Ki yi murmushi kamar yadda kika saba. Kuma idan wata rana kika tuna da ni, ki tuna da ni a matsayin wanda ya taɓa sonki da gaske. Ni kuma zan yi addu'a daga nesa cewa Allah Ya ba ki abin da zuciyarki ke so. 🤲❤️Ba na cewa goodbye saboda na daina son ki… Ina cewa goodbye ne saboda na gaji da riƙe abin da ba ya son ya zauna. ❤️🌹