@abusani566: BABU KARO A TSAKANIN WAHYIN ALƘUR'ANI DA WAHYIN HADITHI GAME DA MAHAIFIN ANNABI: 1. Wasu mutane, ko dai saboda jahiltarsu ga ƙa'idojin da malaman Musulunci suka sanya, ko kuwa saboda bin son zuciyarsu, sai ga shi ido na ganin ido suna riya cewa wai akwai karo da juna, ko kuwa akwai hannun riga, a tsakanin wahyin Alƙur’ani mai girma a cikin suratul Isra'i ayah ta 15: وما كنا معذبين حتى نبعث رسولا da kuma wahyin Hadithi mai daraja: ان ابي واباك في النار; duk kuwa da cewa abin da yake sananne a wurin malaman Musulunci shi ne: sam sam babu ta yadda za a yi a samu yin karo da juna a tsakanin wahyin Alƙur'ani da wahyin Hadithi; dalili kuwa shi ne dukkansu biyun wahyi ne daga Allah MaɗaukakinSarki; yadda haƙiƙanin lamarin yake shi ne: ita Ayar: وما كنا معذبين حتى نبعث رسولا dilalarta dilalah ce a'ammah ta yiwu ta game baban mai tambaya da kuma baban Annabi mai tsira da amincin Allah. To amma shi kuma hadithin: ان ابي واباك في النار dilalarsa dilalah ce khassah wacce take magana kawai a kan mutum biyu kacal, watau baban wanda ya yi tambaya da kuma baban Annabi mai tsira da amincin Allah; saboda haka ko da za a ƙaddara cewa dilalar ayar da shafe su da farkon fari, to dilalah khassah ta hadithin sai ta fitar da su daga ita a'ammar; wannan bayani nawa kuwa dukkan wani mutum mai amsa sunan malamin Musulunci ya san haka yake. Ga wasu misalan wannan bayani namu kamar haka: 2. Hadithin: لا يرث المسلم الكافر ولا الكافر المسلم ya khassase ayar: ولكم نصف ما ترك ازواجكم. Haka nan hadithin: لا تنكح المراة على عمتها ya khassase ayar: فانكحوا ما طاب لكم من النساء. Haka nan hadithin: لا وصية لوارث ya khassase ayar: كتب عليكم اذا حضر احدكم الموت ان ترك خيرا الوصية للوالدين الاقربين. Haka nan hadithin: ليس فيما دون خمس اواق صدقة ya khassase ayar: انفقوا من طيبات ما كسبتم. Akwai wasu nisalan da yawa banda waɗannan da kuka ji. 3. Ke nan kure ne babba wani ya fiskanci mutane ya riƙa ce masu: Ai hadithin: ان ابي واباك في النار ya yi karo da ayar: وما كنا معذبين حتى نبعث رسولا saboda haka za mu yi watsi da hadithin mu koma mu riƙi ayar kaɗai, alhalin kuwa waɗannan wahyi biyu sam sam ba su yi karo da juna ba, a,a, sai dai nau'ukan jahilcinsa ne suke ta karo da juna.

ABU SANI FANDA
ABU SANI FANDA
Open In TikTok:
Region: NG
Monday 14 September 2026 09:43:28 GMT
2058
343
8
4

Music

Download

Comments

islamique1000
islam ☝️💯💯💯💯☪️✅️ :
sallalahu alaihi wasalam
2026-09-14 20:49:44
0
usmandanalmajiri49
USMAN BIN UMAR ASSALAFY .NG.GH :
jazakamullahu kairain
2026-09-14 18:36:30
0
shafiu.hashimu7
Shafiu Hashimu :
💕💕💕
2026-09-14 20:19:05
0
sanikassimsani
Sani kassim Sani :
🥰🥰🥰
2026-09-14 20:08:39
0
user51457210396501
user51457210396501 :
🥰🥰🥰
2026-09-14 18:47:24
0
duniyamakaranta80
duniya makaranta :
❤️❤️❤️
2026-09-14 17:13:03
0
shaykanasstawfiq1
Soufianou Moumouni :
🥰🥰🥰
2026-09-14 17:00:50
0
islamique1000
islam ☝️💯💯💯💯☪️✅️ :
🥰🥰🥰
2026-09-14 20:49:14
0
To see more videos from user @abusani566, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About