@alfajr_college_education: DALIBIN ALFAJR YA ZAMA GWARZON SHEKARA A MUSABAƘAR ALƘUR'ANI TA ƘASA BAKI ƊAYA Alhamdulillah. Babbar nasara ta sake samu ga Alfajr College, bayan da ɗaya daga cikin ɗalibanta, Gwani Mustafa Lawan Hamza, ya zama Gwarzon Shekara a Musabaƙar Alƙur'ani Mai Girma ta Ali Alhuzaifi ta Ƙasa Baki Ɗaya, wadda aka gudanar a Kano a ɓangaren Qira'at. Gwani Mustafa ya fara karatunsa ne da haddar Alƙur'ani Mai Girma a ƙarƙashin Shirin Tajul Waqar, kafin ya ci gaba da zurfafa karatu a fannin Qira'at a Alfajr, har ya kai matsayin ƙwararren malami a wannan fanni. Wannan nasara ta zo ne makwanni bayan da ya lashe Musabaƙar Qira'at ta Jihar Jigawa, lamarin da ke ƙara tabbatar da irin ƙwazo, jajircewa da nagartar da ya nuna a tafiyarsa ta neman ilimin Alƙur'ani. Gwani Mustafa na daga cikin fitattun ɗaliban da Alfajr College ke alfahari da su, kuma wannan nasara wata shaida ce ta ingancin tarbiyya da koyarwar da makarantar ke bayarwa wajen gina ƙwararru masu hidima ga Alƙur'ani da al'ummarsu. Muna taya Gwani Mustafa Lawan Hamza murnar wannan babban rabo, tare da addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara masa ilimi mai amfani, fahimta, ikhlasi da ɗaukaka, Ya kuma sanya wannan nasara ta zama mafarin ƙarin nasarori a hidimar Alƙur'ani Mai Girma. Alfajr Media Alfajr College — Where Genuine Leaders Are Made.

Alfajr college of education
Alfajr college of education
Open In TikTok:
Region: NG
Tuesday 15 September 2026 11:32:08 GMT
7198
1165
9
1

Music

Download

Comments

ayg.textiles.gzw
AYG TEXTILES GZW :
Inason shiga wanga makaranta me albarka
2026-09-15 23:28:39
3
safiyanusule667
safiyanusule667 :
masha Allah
2026-10-29 08:15:01
0
ibraheem_haneef
HANEEF✨💫 :
Allahumma Barik 🤲🏼
2026-09-15 13:48:16
1
fulaniii8
Fulani :
🥰🥰
2026-09-28 12:07:52
1
ibraheem_haneef
HANEEF✨💫 :
🥰🥰🥰
2026-09-15 13:48:00
1
aminahahmad004
Amirah ❤️ :
😁😁😁
2026-10-11 23:04:28
0
To see more videos from user @alfajr_college_education, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About