@malikiyyamediahub: Rt. Hon. Abdulmalik Sarkin Daji ya shiga cikin tawagar jami’an tsaro ta haɗin gwiwa, da suka haɗa da Sojoji, ‘Yan Banga da ‘Yan Sa-kai, domin tunkarar ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane da ke addabar yankunan Kumbashi, Kakihum, Maburya da Shadadi. Malikiyya, tare da Hon. Aliyu Bagga da sauran jami’an tsaron da ke cikin tawagar, sun isa garin Shadadi, inda suka jajantawa al’ummar garin tare da tabbatar musu da cewa za a ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin dawo da zaman lafiya da tsaro. Daga nan, tawagar ta isa Bangi, inda suka ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira tare da isar da saƙon Gwamnan Jihar Neja, tare da tabbatar wa al’ummar yankin cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an kawar da barazanar ‘yan fashin daji, domin ‘yan gudun hijirar su samu damar komawa gidajensu cikin aminci da kwanciyar hankali. Allah Ya ba jami’an tsaro nasara a wannan aiki, Ya kare su, Ya dawo da su lafiya, Ya kuma dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan Kumbashi, Kakihum, Maburya da Shadadi. Amin.

malikiyyamediahub
malikiyyamediahub
Open In TikTok:
Region: NG
Sunday 20 September 2026 22:03:55 GMT
2115
239
7
7

Music

Download

Comments

naseerummar
Naseer Sarkin zabarmawa :
Masha Allahu Sagabanka inda kakeso wallahi ba'abunda zaisaka dominkuwa kawai Addu'ar iyaye ataredakai dan Hajiya dan sarkin daji Saita Allah bata mutunba Fatan Alkairi oga
2026-09-21 01:15:08
0
adamu.kabir6
Adamu Kabir :
Masha Allah kagama lafiya malikiyya amana sarkin daji uban marayu Allah yaima gwamnan Nija state alfarman manzan Allah s a W Ameen fatan alkairi gareka my oga boss Allah yayriko dahannun kah 🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰😭😭😭😭😭😭
2026-09-20 22:30:48
0
yahuzabobi
YahuzaBobi :
masha Allah Allah yasa mudace
2026-09-20 22:18:00
0
babawo.manaja
babawo Manaja :
bamayi
2026-09-20 22:33:26
0
kumbashii
S boda kumbashi :
Masha Allah
2026-09-20 22:09:49
0
dan.juma.sarki1
Dan juma sarki :
🥰
2026-09-21 05:31:20
0
youssouf_amv
Yusuf m namalam :
uban marayu malikiyya amana fatan alkhairi kodayaushe 💯🌹🌹🌹
2026-09-20 22:28:33
0
To see more videos from user @malikiyyamediahub, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About